Hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) a jihar Kano ta bayyana cewa akwai katin zaɓe na dindindin (PVC) sama da 367,000 da jama’a ba su karɓa ba

0 650

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) a jihar Kano ta bayyana cewa akwai katin zaɓe na dindindin (PVC) sama da dubu 367,000 da jama’a ba su karɓa ba har yanzu a jihar.

Kwamishinan INEC na Kano, Ambasada Abdu Zango, ya bayyana haka ne yayin da ya karɓi tawagar kwamitin gwamnatin jihar kan rajistar katin zaɓe ƙarƙashin jagorancin kwamishinan yaɗa labarai, Ibrahim Abdullahi Waiya.

Ya yabawa matakin kafa kwamitin tare da kira ga mambobinsa da su ƙara ƙaimi wajen wayar da kan jama’a domin su tafi su karɓi katin zaɓensu.

Zango ya ƙara da cewa jihar Kano tana da masu zaɓe sama da miliyan 6 da aka riga aka yi wa rajista, wanda fiye da miliyan 3.6 daga cikinsu ke cikin ƙananan hukumomin birnin Kano.

Waiya cewa kwamitin zai ci gaba da amfani da dabaru wajen motsa jama’a domin yin rajista da kuma karɓar katin zaɓensu.

Leave a Reply