Ƙungiyar Likitoci A Birnin Tarayya Abuja Ta Fara Yajin Aikin Gargadi Na Tsawon Kwanaki Bakwai

0 669

Ƙungiyar likitoci a birnin tarayya Abuja ta fara yajin aikin gargadi na tsawon kwanaki bakwai saboda matsalolin dake damun fannin kiwon lafiya a birnin.

Shugaban ƙungiyar, George Ebong, ya ce rashin isassun ma’aikata, da kayan aiki marasa kyau, da jinkirin biyan albashi da alawus sun haddasa gagarumin cikas ga tsarin lafiya.

Likitocin sun yi gargadi cewa idan gwamnati ta ci gaba da sakaci, da sagegeduwa hakan na iya haddasa rugujewar tsarin kiwon lafiya gaba ɗaya, yayin da su kansu suke fama da aiki a sassa da dama lokaci guda.

Ƙungiyar ta baiwa gwamnatin babban birnin tarayya wa’adin mako guda ta dauki matakan gyara, musamman a fannin walwala da kayan aiki, ko kuma su ci gaba da tsawaita yajin aikin.

Leave a Reply