Ƴan sanda 11 za su amsa tuhuma a kotu kanya bisa zargin da ake musu a kan kisan jaririya a Kenya

0 496

Ana sa ran ’yan sanda 11 a Kenya za su bayyana a kotu a yau domin amsa tuhuma kan kisan jaririya Pendo mai watanni shida, a lokacin tashin hankalin da ya biyo bayan zaɓen 2017.

Ana tuhumar jami’an da laifuka 47, ciki har da laifukan cin zarafin ɗan Adam, bisa zargin jagorantar hare-haren jami’an tsaro da suka yi sanadiyyar kisan jaririyar bayan zaɓen da aka ce ya samu rigima.

An jinkirta shari’ar sau da dama, inda lauyoyin waɗanda abin ya shafa ke zargin gwamnati da yin jinkiri ka shari’ar

Leave a Reply