Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya ce Allah ya amsa addu’ar da ya yi na samun damar ci gaba da jagorantar kasar.
Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, yayin da yake tsokaci kan ziyarar Umrah da ya kai kasar Saudiyya, inda Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud ya ba shi dama ta musamman ta shiga cikin dakin Ka’aba tare da tawagar Najeriya domin gudanar da addu’a.
Shugaban ya gode wa Sarkin Saudiyya da Yarima mai jiran gado, Mohammed bin Salman, bisa damar da suka ba shi na shiga dakin Ka’aba.
Ya bayyana damar a matsayin wata muhimmiyar kyauta ta addini da ba zai manta da ita ba.
Tinubu ya ce a lokacin addu’arsa a cikin Ka’aba, ya roki Allah ya ba shi hikima da juriyar ci gaba da yi wa al’ummar Najeriya hidima, yana mai cewa ya yi imanin an amsa addu’arsa.
Ya kuma yi nuni da cewa mulki amana ne daga Allah, wanda yake bayar da shi ga wanda ya so, kuma yana karbe shi a duk lokacin da ya so.
Shugaban ya ce wannan imani ya kara masa kwarin gwiwar ci gaba da gudanar da ayyukan raya Najeriya, yana mai cewa jajircewarsa wajen gina kasar ta kara karfi.
Dangane da tattalin arziki, Tinubu ya bayyana kyakkyawan fata kan ci gaban da ya ce an samu a karkashin gwamnatinsa, yana mai cewa kasar ta fara fita daga mawuyacin halin tattalin arziki.
Ya kuma jaddada bukatar zuba jari a makomar matasa, yana mai cewa matakan da shugabanni ke dauka a yanzu za su shafi yadda al’umma za ta tuna da su nan gaba.