Jigawa: Magoya Bayan Tinubu Sun Fara Gangamin Neman Wa’adin Mulki Na Biyu

0 12

Magoya bayan Shugaba Bola Tinubu a Jihar Jigawa sun gudanar da gangamin neman sake zabensa a 2027, inda suka rika rera taken “Tinubu Must Stay” yayin bude ofishin yakin neman zabe a Garun Gabas, karamar hukumar Malam Madori.

Daraktan Hukumar Bunkasa Fasahar Sadarwa ta Kasa (NITDA), Kashifu Inuwa Abdullahi, ne ya jagoranci gangamin, wanda ya samu halartar shugabannin APC, masu ruwa da tsaki, mata da matasa.

A yayin taron, wasu mambobin jam’iyyun PDP da NDC sun sanar da ficewa daga jam’iyyunsu zuwa APC.

Kashifu Inuwa, wanda shi ne shugaban kwamitin amintattu kuma kodinetan kungiyar Tinubu Movement for Sustainable Governance Foundation (TMS), ya ce kungiyar na kafa rassanta a matakin kananan hukumomi da unguwanni domin wayar da kan al’umma game da manufofi da sauye-sauyen gwamnatin Tinubu.

Ya ce ilimi, noma, samar da abinci, tsaro, fasahar zamani da kiwon lafiya na daga cikin muhimman bangarorin da gwamnati ke kokarin ingantawa.

Ya bukaci al’ummar Jigawa su fito kwansu da kwarkwatarsu domin tabbatar da nasarar Tinubu a zaben 2027, yana mai cewa ci gaba da mulkinsa zai ba shi damar kammala shirye-shiryen raya kasa.

Daraktan NITDA ya kuma bayyana shirin tallafa wa wasu mata 200 a Garun Gabas, ta hanyar shirye-shiryen karfafa tattalin arzikin al’umma.

Ya ce a wasu shirye-shiryen da suka gabata a Jigawa, ciki har da Hadejia, an bai wa mata tallafin kudi, injinan dinki, kayan aikin yin burodi da kayayyakin noma domin bunkasa sana’o’insu.

A nasa bangaren, shugaban APC na karamar hukumar Malam Madori, Alhaji Tanko Ahmad, ya yabawa NITDA bisa kafa cibiyar koyar da fasahar sadarwa a makarantar sakandaren gwamnati ta Garun Gabas.

Shi ma mai jagorantar kungiyar TMS a Garun Gabas, Injiniya Hashim Suleiman, ya ce yadda jama’a suka halarci taron na nuna karuwar karbuwa da kungiyar ke samu.

An kuma karrama Kashifu Inuwa da lambar yabo bisa gudunmawarsa wajen bunkasa fasahar zamani da wayar da kan al’umma.

Bude ofishin na daga cikin shirin kungiyar na kafa rassanta a fadin jihohi da kananan hukumomi domin karfafa goyon bayan Tinubu gabanin zaben 2027.

Leave A Reply

hitta mer om recensioner