Babu maganar sulhu wajen magance rikicin tsaro

0 238

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya nemi goyon bayan ‘yan Najeriya kan shirin da gwamnatin tarayya da za ta bullo da shi nan ba da dadewa da zai magance rikicin dake faruwa a yankin Arewa maso Yamma.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya ruwaito cewa yankin na fama da karuwar ‘yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane wadanda suke yin sanadiyar mutuwar daruruwan mutane tare da raba wasu dubbai da matsugunansu.

Ya kuma kara da cewa yanzu haka masu ruwa da tsaki da dama suna ta kiraye kirayen a dauki wani salo na dabarun soji domin maganin rikicin.

Sai dai rahotanni sun ce babban hafsan sojin kasa, Manjo Janar Taoreed Lagbaja, ya yi fatali da matakin yin afuwa ga ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda a kasar a makon jiya, yana mai cewa maimakon su a sulhunta su tu ba, batagarin zasu yi amfani da wannan damar wajen yada kungiyyar su da kai hari ga ‘yan kasar da ba su ji ba ba su gani ba.

Sai dai da yake magana jiya a Kano, mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya ce shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kuduri aniyar daukar matakin da ya dace da tsarin mulkin zamani. Ya ce babu maganar sulhu wajen magance rikicin yankin Arewa maso Yamma.

Leave a Reply

%d bloggers like this: