0 301

Ƙungiyar Likitocin da ke yin aiki a asibitocin koyarwa da na musamman (NARD) ta bayyana cewa za ta fara yajin aiki na sai-baba-ta-gani daga ranar Juma’a, 31 ga Oktoba 2025, da ƙarfe 11:59 na dare.

Shugaban ƙungiyar, Dr. Mohammed Usman Suleiman, ya bayyana haka a wata sanarwa bayan taron gaggawa na awanni biyar da majalisar zartarwa na ƙasa na ƙungiyar ya gudanar.

Ya ce matakin ya biyo bayan ƙarewar wa’adin kwanaki 30 da suka bai wa gwamnatin tarayya don magance buƙatun su, ciki har da:

  1. Biyan bashin alawus-alawus da aka tara,

2. Sake duba tsarin albashi (CONMESS),

3. Sake dawo da likitocin da aka kora a asibitin koyarwa na Lokoja,

4. Da kuma inganta yanayin aiki.

Dr. Suleiman ya zargi wasu jami’an gwamnati da yin shiri na zaluntar likitoci, inda ya bukaci mambobinsu da su tsaya tsayin daka wajen kare muradunsu.

Ƙungiyar ta kuma umarci dukkan likitoci mambobinta su yi shiri ta hanyar mika marasa lafiya da ke hannunsu kafin fara yajin aikin.

Ana sa ran wannan yajin aikin zai shafi ayyukan lafiya a asibitocin koyarwa da na musamman a faɗin ƙasar.

Leave a Reply