Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta tarwatsa wani biki da ake zargin auren maza da maza a wani wurin taro da ke Hotoro Bypass, a Karamar Hukumar Tarauni ta jihar.
Rahoton ya bayyana cewa jami’an Hisbah sun kai samame ne da yammacin Asabar bayan samun bayanan sirri daga wani mai kishin al’umma cewa wani matashi mai suna Abubakar Idris yana shirin yin aure da wani saurayi.
Da jami’an Hisbah suka isa wurin, sun tarar da ana gudanar da taro cikin duhu, inda suka kama mutum 25 da ke wurin – ciki har da ’yan daudu 18 da mata 7 daga sassa daban-daban na Kano, kamar Sheka, Yar Gaya, da Kofar Nasarawa.
Mataimakin Kwamandan Hukumar, Dakta Mujahid Aminuddeen Abubakar, ya ce an kai wadanda aka kama ofishin Hisbah don ci gaba da bincike, kuma za a gurfanar da su gaban kotu nan ba da jimawa ba.
Ya roƙi iyaye su kula da tarbiyyar ’ya’yansu, tare da yin kira ga jama’a su rika sanar da hukumomi idan sun ga wani abu da ya saba wa tarbiyya da dokokin Musulunci.