Kwamitin haɗin gwiwar Majalisar Dattawa da ta Wakilai kan sauya kundin tsarin mulki ya amince da buƙatar ƙirƙirar sabbin jihohi guda shida a faɗin ƙasar.
Wannan shawara ta fito ne bayan taron kwanaki biyu da aka gudanar a Legas, ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, da takwaransa na Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu.
Kwamitin ya duba buƙatu 69, ciki har da neman kafa jihohi 55 da ƙananan hukumomi 278.
Da zarar an amince da shawarwarin, Najeriya za ta koma tana da jihohi 42 maimakon 36 da ake da su yanzu.