Aƙalla Mutane 15 Suka Rasu Sakamakon ɓullar Cutar Ebola A Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo

0 741

An samu rahoton mutuwar mutum aƙalla 15 sakamakon ɓullar cutar Ebola a lardin Kasai na Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, inda aka tabbatar da ƙarin mutum 43 sun kamu da cutar.

Daga cikin wadanda cutar ta shafa akwai ma’aikatan lafiya huɗu, kuma hukumomi sun tabbatar cewa nau’in Zaire strain ne ya haddasa barkewar.

Ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano asalin ɓullar cutar, yayin da hukumar lafiya ta Afirka (Africa CDC) ta ƙaddamar da martanin gaggawa tare da hadin gwiwar Hukumar Lafiya ta Duniya, wacce ta tura tan 12 na kayan agajin gaggawa da na’urorin lafiya.

Shugaban Africa CDC, Dakta Jean Kaseya, zai isa ƙasar domin haɗa kai da ma’aikatar lafiya wajen jagorantar matakan gaggawa

A babban birnin Kinshasa, ana yi wa ma’aikatan gaggawa allurar rigakafi, tare da ɗaukar matakan rufe makarantu da kasuwanni domin daƙile yaduwar cutar.

Ƙasashe da dama ciki har da Uganda da Sudan ta Kudu da Najeriya sun sanar da fara sa ido kan cutar Ebola.

Wannan shi ne karo na 16 da aka samu ɓarkewar cutar a DR Congo, yayin da lardin Kasai ne ya fuskanci ɓullewar cutar a karon karshe a shekarar 2008.

Leave a Reply