Abdul Samad Rabiu BUA ya sha alwashin ci gaba da rage farashin shinkafa da sauran kayan abinci

0 209

Duk da cewa rahoton sabuwar kididdigar hauhawar farashi da Hukumar NBS ta fitar ya nuna sauki a matakin ƙasa, jihohi goma da babban birnin tarayya Abuja na ci gaba da fama da hauhawar farashi da ya haura kashi 30 cikin 100, inda jihar Enugu ta fi muni da hauhawar da ya kai kashi 36.

Rahoton na watan Afrilu ya nuna cewa hauhawar farashi ya sauka zuwa kashi 23.71 cikin 100 daga 24.23 na watan Maris, amma jihohi kamar Kebbi, Neja, Benue da sauran su na ci gaba da fuskantar matsin tattalin arziki, musamman ta fuskar abinci.

A jihar Benue, rahoton ya nuna cewa farashin abinci ya tashi da fiye da kashi 51, lamarin da ke da nasaba da rashin tsaro da ke hana noma gudana yadda ya kamata. Sai dai a wani yunƙuri na rage tsadar kayan masarufi, shugaban rukunin kamfanonin BUA, Abdul Samad Rabiu, ya sha alwashin ci gaba da rage farashin shinkafa da sauran kayan abinci, yana mai bayyana matakin gwamnatin Tinubu na dakatar da kudin fito kan kayan abinci a matsayin babban sauƙi da ya tilasta wa masu ɓoye kaya su fitar da su kasuwa a farashi mai rahusa.

Leave a Reply