Gwamnatin jihar Anambra ta haramta raba kayan abinci da sauran kyaututtuka ga mabarata a tituna da wuraren taruwar jama’a
.
Gwamnatin jihar ta ware musamman karkashin gadar Aroma da ke Awka, babban birnin jihar, da sauran wurare a matsayin manyan wuraren da ta hana wannan dabi’a.
Haka kuma, gwamnatin jihar ta haramta kowace irin bara, yawo ba gaira ba dalili da kuma kasuwanci a kan titi a karkashin gadar Awka, tana mai cewa wannan mataki ya zama dole don kare mutunci da tsari na babban birnin, wanda ke wakiltar fuskar jihar.
Wata sanarwa da Darakta Janar kuma Shugaba na Hukumar Raya Birnin Babban Birnin Jihar Anambra Anambra State Capital Territory Development Authority, Ossy Onuko, ya fitar, ta bayyana cewa wannan umarni na daga cikin kokarin gwamnati na tsaftace birnin da kuma tabbatar da doka da oda.
Onuko ya ce duk wanda aka samu da karya wannan umarni za a kama shi tare da gurfanar da shi a gaban kotu.