Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya amince da daukar sabbin jami ai 130, 000 da zasu kare dazukan Nijeria
Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya amince da Samar da wani tsari na kare dazukan kasar domin magance yaduwar rashin tsaro a fadin kasar.
Haka kuma, Shugaba Tinubu ya umurci gwamnonin jihohi da su dauki akalla mutane 2000 zuwa 5000 gwrgwadon ikonsu domin tsare dazuka 1,129 da ke akwai a kasar.
Shugaban Kasa ya amince da haka ne a taron majalisar zartaswa da ya gudana a ranar Litinin din da ya gabata.
Horar da Sababbin jami’an zai kasance a karkashin kulawar ofishin mai ba Shugaban Kasa Shawara Kan harkar tsaro da kuma Ma’aikatar muhalli.