Najeriya ba za ta koma mulkin soja ba – Yakubu Gowon

0 148

Tsohon shugaban ya ce dimokuraɗiyya ita ce turbar samar wa Najeriya ci gaba mai ɗorewa.

Tsohon Shugaban Ƙasa, Janar Yakubu Gowon (mai ritaya), ya ce Najeriya ba za ta sake komawa mulkin soja ba.

Ya bayyana haka ne a Babban Birnin Tarayya, Abuja yayin ƙaddamar da littafi mai suna “Military Factor in Nigerian History, 1960-2018”, domin murnar cika shekaru 70 da kafa ƙungiyar Tarihi ta Najeriya (HSN).

Gowon ya ce duk da irin gudunmawar da sojoji suka bayar a tarihin Najeriya, musamman a lokacin yaƙin basasa da kuma samar da ababen more rayuwa bai kamata su sake tsoma baki a siyasa ba.

Ya jaddada cewa dimokuraɗiyya, duk da kurakuran da ake samu a cikinta, ita ce hanya mafi dacewa don ci gaban ƙasa.

“Ya kamata zamanin mulkin soja ya ƙare a Najeriya. Duk da gazawar dimokuraɗiyya ita ce hanya mafi kyau wajen ci gaban ƙasa da kuma bai wa mutane dama su shiga harkokin mulki,” in ji Gowon.

Ya amince cewa a wasu lokuta a mulkin soja ya tauye ’yancin jama’a kuma ya hana dimokuraɗiyya ci gaba.

Sai dai ya ce, idan aka amince da kuskuren da aka yi a baya, za a samu ingantaccen tsarin siyasa a gaba.

“Mulkin soja ya zo da ci gaba da kuma raɗaɗi. Don mu samu ci gaba, dole ne mu karɓi gaskiya game da abin da ya faru a baya, mu gyara gaba,” in ji shi.

Leave a Reply