Kotu ta yankewa tsohon shugaban Maurtania wa’adin zaman gidan kaso

0 136

Kotun ɗaukaka ƙara a Mauritania ta zartaswa tsohon shugaban ƙasar Mohamed Ould Abdel Aziz ɗaurin shekaru 15 a gidan kaso, bayan da ya ɗaukaka ƙara akan hukuncin ɗaurin shekaru biyar da aka yanke masa, bisa aikata laifin karkata wasu kuɗaɗe shekaru biyu da suka gabata.

Tsohon shugaban, wanda ke ɗaure a gidan kaso tun hukuncin farko da aka yanke masa a watan Janairun 2023, ya bayyana a gaban kotu ne tare da ƙusoshin gwamnatinsa da suma ke fuskantar tuhume-tuhume akan amfani da matsayi wajen wadaƙa da dukiyoyin al’umma.

Har’ila-yau kotun dake zamanta a babban birnin ƙasar Nouakchott ta tabbatar da hukuncin karɓe ilahirin kadarorin tsahon shugaban tare da daƙile dukkanin haƙoƙinsa a matsayin ɗan kasa.

Wani wakilin Kamfanin dillanci labarun Faransa AFP ya bayyana cewa da jin wannan hukuncin sai tsohon shugaban na Mauritania Aziz, mai shekaru 68, ya kasance tamkar maraya.

Masu bincike dai sun yi kiyasin cewa Aziz, wanda ya shugabanci ƙasar dake Arewa maso gabashin Afirka mai adadin mutane miliyan 4.5 na tsawon sama da shekaru goma, ya mallaki kadarori da tarin dukiya da ta kai Dala miliyan 70 a lokacin mulkinsa.

An kuma yanke masa hukuncin farko na ɗaurin shekaru biyar a gidan yari ne bayan da aka sameshi da laifin halatta kuɗin haram a watan Disambar shekarar 2023. 

Leave a Reply