Labarai

Abubakar Malami: Gwamnatin Tarayya ta fara tattara sunayen mutanen da ake zargi da tallafawa ta’addanci a Najeriya

Babban Lauyan Gwamnati kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami ya ce Gwamnatin Tarayya ta fara tattara sunayen mutanen da ake zargi da tallafawa ta’addanci a Najeriya da nufin gurfanar da su a gaban kuliya.

Ya bayyana hakan ne ranar Juma’a a Abuja lokacin da yake amsa tambayoyi daga ’yan jaridar Fadar Shugaban Kasa.

A cewarsa, binciken wanda yanzu haka yake gudana ya fara samar da gamsassun hujjoji domin gurfanar da wadannan fitattun mutanen da kuma kungiyoyi a fadin kasa.

Malami ya ce kamen wasu wadanda ake zargi a ’yan kwanakin nan ya biyo bayan yanke wa wasu ’yan Najeriya hukunci kan taimaka wa ta’addancin a Hadaddiyar Daular Larabawa DUBAI.

A cewarsa sun gano cewa akwai kwararan hujjoji dake alakanta wasu fitattun ’yan Najeriya da dama da tallafawa harkar ta’addanci da kudade, kuma suna tattara sunayensu domin gurfanarwa a gaban kotu.

To sai dai Ministan ya ki amincewa Ya fadi adadin wadannan mutanen da ake tattarawa.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: