Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Kan Ranar Hausa Ta Duniya

0 141

A duk ranar 26 ga watan Agusta ne ake bikin ranar Hausa ta duniya. Ana amfani a ranar ne dai wajen nuna alfahari da harshen tare da raya shi da kuma inganta shi.

Tun a cikin shekarar 2015 ne dai aka fara gudanar da wannan rana, wato wannan kenan shi ne karo na biyar.Sai dai abu ne mai wuya a iya tantancewa, fayyacewa ko kuma sahihance asalin harshen Hausa da lokaci ko jinsi da al’ummar da suka fara yin amfani da shi.

Sai dai kuma hakan bai hana manazarta, masana, masu bincike da kuma manyan malamai rika yin kirdado da kintacen kokarin gano asalin Hausa ba.Harshen Hausa na daya daga cikin harsunan da ke yado, ba a nan Najeriya kadai ba, har ma a cikin kasashen Afrika ta Yamma da wasu kasashe da dama.

Ta ko wane fanni za a iya cewa Hausa ta samu karbuwa a duniya, idan aka yi la’akari da hanyoyin zamani na isar da sakonni, ilmantarwa da fadakarwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: