Muhimman Batutuwa Kan Cikar Jigawa Shekaru 28 Da Kafuwa

0 117

A Yau ne jihar Jigawa tayi bikin cika shekaru 28 da kafa ta.


An dai kafa jihar ta Jigawa ne a ranar 27 ga watan Agustan shekarar 1991, a lokacin da gwamnatin mulkin soje ta kara adadin jihohi guda 9 a fadin Najeriya, wanda adadin su ya zama guda 30 cif a wancan lokacin karkashin shugaban kasa General Ibrahim Babangida mai ritaya.


Sanarwar ta samu goyon bayan wata dokar soje ta 37 a shekarar 1991.


An yanko jihar ne daga jihar kano wanda take da fadi murabbain kilomita 22,410.
A bangaren gabas jihar tayi iyaka da jihar Bauchi da Yobe, ta bangaren yamma tayi iyaka da jihar Kano, yayin da kuma daga arewa tana iyaka da jihar Katsina da Yobe da kuma Jamhuriyar Nijar.


Mafiya yawan al’ummar Jihar Jigawa sun hada da hausa Fulani, da Mangawa da Badawa da kuma Ngizimawa wadanda yawancinsu bare bari ne.


Jihar mai babban birnin a Dutse ta kunshi kananan hukumomi 27, da mazabun majalisar dattawa guda uku, da mazabun majalisar tarayya guda 11 da kuma na majalisar jiha guda 30 kamar yadda kundin tsarin mulki kasarnan na 1999 ya tanadar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: