Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, ya jagorancin zaman kwamitin tattalin arziki a wannan zangon na biyu na shugaban kasa Muhammadu Buhari, mai taken kudirorin Next Level akan Kasafin Kudi.
Cikin wadanda suka halarci zaman sun hada da Ministar Kudi, da Ministan Kasafin Kudi da Tsare-Tsare, da Ministan Masana’antu, da Ministan Kasuwanci da Zuba Jari, da Ministan Labarai da Al’adu, da Ministan Ayyuka da Gidaje, da Karamin Ministan Kasafin Kudi da Tsare-Tsare, da kuma Karamin Ministan Man Fetur.
Karin wadanda suka halarci zaman akwai Gwamnan Babban Bankin Kasa, CBN, Shugaban Kamfanin Fetur na Kasa, NNPC, da Shugaban Hukumar tara kudaden shiga, da sauransu.
Zaman ya fara da bibiyar aiwatar da kasafin kudi na shekarar 2019.