EFCC Zata Bankado Karin Wasu Masu Aikata Laifi

0 160

Hukumar Yaki da masu yiwa tattalin arziki zagon kasa ta EFCC tace za a gano karin wasu masu laifi, kasancewar ana cigaba da bincike akan ‘yan Najeriya 80 da hukumar binciken kasar Amuka ta zarga da laifufukan dake alaka da yanar gizo.

Shugaban Ofishin EFCC na Ibadan, Mista Friday Elebo, shine ya shaidawa manema labarai a Ibadan cewa hukumar ta fara bincike akan ‘yan Najeriyan da hukumar binciken kasar Amuka ta zarga da laifufuka.

Friday Elebo yace hukumar na aikin hadin gwiwa da wasu hukumomin kasa da kasa dake makamancin wannan aiki, musamman hukumar binciken kasar Amuka, wajen dakile laifufukan alaka da yanar gizo, da aika kudade, ba bisa ka’ida ba.

A cewarsa, Hukumar EFCC za ta yi iya kokarin domin tabbatar da cewa an kare martabar ‘yan Najeriya dake aiki tukuru tare da bin doka da oda.

Friday Ebelo yace an san ‘yan Najeriya da basira, da aiki tukuru da kuma kokari, inda yace an tabbatar da hakan ta dumbin nasororin da suke samu a ko’ina a fadin duniya.

Shugaban ofishin na EFCC yace, daga watan Janairun wannan shekara zuwa yanzu, ofishinsa ya kama mutane 263 da ake zargi da laifufukan dake alaka da yanar gizo, cikinsu mutane 111 a yanke musu hukunci tare da kulle su a gidajen yari.

Friday Ebelo sai yayi kira ga iyaye da suke fadakar da ‘ya’yansu akan sakamakon aikata laifi, domin su kauracewa aikatawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: