Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ta zargi Majalissar Tarayya da ke karkashin rinjayen APC da gangan suka jinkirta amincewa da Kudirin Dokar Zaɓe ta 2025, tana mai gargaɗin cewa ci gaba da wannan jinkiri na iya lalata sahihancin zaɓukan gama-gari na 2027.
A cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Juma’a, wadda Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya sanya wa hannu, ADC ta ce jinkirin ya haifar da “manyan shakku” kan yadda Majalissar ke da niyyar aiwatar da sauye-sauyen zaɓe da aka tsara domin hana maguɗi.
“Ci gaba da ja da baya da Majalissar Tarayya ke yi kan Kudirin Dokar Zaɓe ta 2025 na haifar da shakku cewa Majalissar, wadda APC ke da rinjaye a cikinta, da gangan take jinkirta muhimman gyare-gyare—musamman waɗanda aka tsara domin sa maguɗin zaɓe ya zama da wahala a nan gaba,” in ji ADC.
Jam’iyyar ta nuna damuwa kan cewa wasu daga cikin gyare-gyaren da aka gabatar a cikin Dokar Zaɓe ta 2022 suna ƙunshe da sabbin ƙa’idojin bin doka da sharuddan cancanta ga jam’iyyun siyasa, tana mai jaddada cewa rashin isasshen lokaci da nazari da aiwatar da su ka iya haifar da mummunan sakamako.
“Rashin ba da isasshen lokaci da nazari wajen aiwatar da waɗannan tanade-tanade na iya haifar da munanan sakamako ga jam’iyyun siyasa da kuma Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC),” in ji Abdullahi, yana ƙara da cewa rashin fayyace ƙa’idoji na iya zama “tarko” ga jam’iyyun adawa tare da wahalar da shirin INEC.
ADC ta kuma ambaci tanade-tanaden da ke wajabta tantance masu kaɗa ƙuri’a ta na’ura (e-voting accreditation) da kuma aikawa da sakamakon zaɓe ta na’ura (electronic transmission), tana mai cewa waɗannan su ne mafi ƙarancin abubuwan da ake buƙata domin sahihin zaɓe.
A cewar jam’iyyar, tanadin da ke wajabta INEC ta fitar da sanarwar zaɓe akalla kwanaki 360 kafin zaɓen gama-gari ya sa jinkirin ya fi tayar da hankali.
“Ko yanzu ma, lokaci ya yi ƙanƙanta ƙwarai don shiri da bin ƙa’idoji yadda ya kamata,” in ji sanarwar.
Jam’iyyar ta yi kira ga Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai da su amince da kudirin ba tare da ƙarin jinkiri ba, tana mai gargaɗin cewa duk wani ƙarin jinkiri na iya rage amincewar jama’a da tsarin zaɓe.
“Duk wani jinkiri na barazana ga sahihancin zaɓukan 2027 kuma yana rushe amincewa da tsarin zaɓe gaba ɗaya. Najeriya ba za ta iya jure wani zaɓe mai rikici ko shakku ba,” in ji ADC.
Haka kuma, ADC ta roƙi ƙungiyoyin fararen hula, abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa, da sauran jam’iyyun siyasa da su matsa lamba kai-tsaye kan Majalissar Tarayya domin ta yi gaggawar ɗaukar mataki.