Aminu Ado Bayero Ne Ya Kamata Ya Ci Gaba da Zama Sarkin Kano

0 140

A cewarsa, batun na iya warwarewa ne kawai ta hannun Kotun Koli.

“Abin da muke yi kawai shi ne jiran Kotun Koli ta yanke hukuncinta,” in ji shi. “Ban san da wata yarjejeniya ta sulhu ba, ko kuma wa zai fara irin wannan tsari—ko gwamnatin jiha ce ko kotu.”

Ya jaddada cewa babu wata yarjejeniya da za ta kwace Aminu Ado Bayero ko kuma iyalan Ado Bayero sarautar Kano.

“Ganin yadda nake kallon lamarin, babu wata yarjejeniya da za ta karɓe masarautar daga hannun Aminu Ado Bayero ko iyalinsa,” in ji Danagundi.

Har ila yau, ya yi watsi da ra’ayoyin da ke cewa ana iya janye shari’ar saboda daidaituwar siyasa tsakanin Gwamnatin Jihar Kano da Gwamnatin Tarayya.

“Wasu na ganin tunda gwamnan yanzu yana tare da Gwamnatin Tarayya, kowa zai amince a bar shari’ar—amma hakan ba gaskiya ba ne,” in ji shi.

Danagundi ya kuma ambaci mulkin marigayi Sarkin Kano Ado Bayero, wanda ya yi mulki tsawon shekaru fiye da hamsin ba tare da tabo ba, yana mai jaddada cewa bai kamata a watsar da gadonsa ba.

“Ɗansa ya fi cancanta ya gaji sarautar Sarkin Kano, maimakon wani daga wani gida dabam,”.

Leave a Reply