Gwamnatin Bauchi Ta Gano Ma’aikatan Bogi 3,000, Gamida Ceto Kudin Jihar Fiye da Naira Biliyan Huɗu

0 260

Gwamnatin Jihar Bauchi ta ce ta gano tare da cire ma’aikatan bogi sama da 3,000 dake karban albashin gwamnati, lamarin da ya ceto kudin jihar fiye da Naira biliyan huɗu.

An gano hakan ne a wani taron musamman na Kwamitin Kula da Tattalin Arzikin Jihar da Gwamna Bala Mohammed ya jagoranta a Fadar Gwamnati da ke Bauchi.

Bayan taron, Shugaban Ma’aikatan Jihar, Muhammad Sani Umar, tare da Babban Mashawarcin Tattalin Arziki ga gwamna, Yahuza Adamu Ningi, sun ce an sake duba tsarin biyan albashi gaba ɗaya.

Ningi ya bayyana cewa gwamnatin ta yi aikin tantance albashi tare da kamfanin Onyx Investment Advisory Limited, wanda ya kai ga gano gamida cire ma’aikatan bogin.

Ya ce tun daga lokacin da gwamnati ta karɓi biyan albashi a watan Agustan 2024, an daina koke-koke, kuma sabon tsarin ya ceci Naira biliyan 4.16 da ake asara a baya.

A gefe guda, Umar ya ce kwamitin ya amince da biyan alawus na wata-wata ga limaman masallatan Juma’a da fastocin coci-coci a faɗin jihar ba tare da la’akari da mazhaba ba.

Sai dai jam’iyyar PRP a Bauchi ta gargaɗi gwamnatin da ta guji siyasantar da addini.

Leave a Reply