Aisha Buhari Tayi Nata Bikin Dimukuradiyyar Cikin Sabon Salo

0 113

A yau Laraba Najeriya ke bikin ranar dimokaradiyya 12 ga watan Yunin shekarar 2019, Uwar gidan shugaban Kasa Aisha Buhari,ta jagoranci wasu matan shugabanin Afrika zuwa Yola jihar Adamawa, domin bude wata cibiyar kula da mata masu juna biyu da kuma kaddamar da wani sabon shiri na rage talauci ga al’ummar karkara, karkashin hukumar samar da aikin yi ta NDE.

A cikin jawabin Aisha Buhari, ta ce “A madadin sauran matan shugabanin Afrika biyar da suka zo don taya Najeriya da yan Najeriya murnar ranar dimokaradiyya, uwar gidan shugaban kasar Ghana Madam Rabecca Akufo Addo,ta ce matan shugabanin kasashen Afrika kan taka rawa ta fannonin ci gaba duk da cewa basu da wani kasafin kudi da akan basu.

Ta kuma yabawa Aisha Buhari, bisa wasu ayyuka da ta kirkiro na ci gaban al’umma. Ita ma a jawabinta, uwar gidan shugaban Najeriya Aisha Buhari, ta ce gidauniyarta ta ‘Future Assured’ za ta ci gaba da hada kai da sauran cibiyoyi don tallafawa al’umma musamman masu karamin karfi.

Dakta Nasir Ladan, dake zama shugaban hukumar ta NDE a Najeriya, ya bayyana manufar wannan shiri da aka kaddamar a Yola.

Leave a Reply

%d bloggers like this: