Rahoton Arangamar Yan sanda da Jama’a Yayin Zanga-zanga a Hong Kong

0 306

Dubban Mutane ne yau Laraba suka sake gudanar da zanga zangar adawa da shirin amincewa da wata doka da zata bada damar tisa keyar wanda ake zargi da aikata laifi daga Hong Kong zuwa China domin yi masa shari’a.

Masu zanga zangar akasarin su matasa da dalibai sun yiwa ofisoshin gwamnati kawanya, inda suka hana motoci motsawa domin ganin Majalisa tayi watsi da dokar.

Ganin yadda tururuwar masu zanga zangar ta mamaye jami’an tsaron da suke cikin damarar ko ta kwana, shugabannin Majalisa sun bayyana dakatar da mahawara kan dokar zuwa wani lokaci nan gaba.

A shekara ta 2017 aka zabi Carrie Lam a matsayin sabuwar shugaba Hong Kong bayan kwamitin da ke goyon bayan China sun kada kuri’ar.

Zaben dai a lokacin ya fuskanci suka daga ‘yan kasar da suke son a ba kowa yancin kada kuri’a, maimakon wasu tsiraru.

Leave a Reply

%d bloggers like this: