

- Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ta rufe kamfanonin ruwa guda 10 a jihar Ondo bisa rashin bin ka’idoji - July 4, 2022
- Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar AA, Hamza Al-Mustapha, ya ce jam’iyyarsa ba za ta yi hadin gwiwa da mutanen da basu damu da makomar al’umma ba - July 4, 2022
- Yadda wani mutum ya kona matarsa bayan ya gama dukanta a jihar Ogun - July 4, 2022
Akalla manoma bakwai ne aka kashe a gonakinsu a kauyen Faru da ke karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara da sanyin safiyar jiya.
Wani dan yankin mai suna Garba Abdullahi ya shaida wa manema labarai cewa wadanda abin ya shafa suna gonakinsu ne a lokacin noman bana inda ‘yan bindigan suka kai musu hari tare da kashe su.
Abdullahi ya bayyana cewa daya daga cikin ‘yan uwan sa Sani Akwala yana cikin manoman da ‘yan fashin suka kashe.
Abdullahi ya ce ‘yan bindigar sun addabi kauyen tun farkon noman damina ta bana.
Ya ce barayin sun sha alwashin cewa babu wani aikin noma da za a yi a yankin a noman bana.
Ya kara da cewa ‘yan bindigar sun zagaya gonaki domin tabbatar da bin umarninsu.
Ya koka da cewa zai yi wuya manoma su yi noma a bana, yana mai kira ga hukumomin da suka dace da su gaggauta yin wani abu.