Labarai

Har yanzu babu tabbacin adadin wayanda suka ji raunika a zanga-zangar da akai a Sakkwato bisa batanci ga Manzon Allah

Akalla mutum daya ne ya mutu yayinda wasu da dama suka samu raunuka a jiya yayin da ‘yan sanda ke kwantar da tarzomar da ta barke bayan da wasu gungun jama’a ke zanga-zanga a Sokoto domin neman a sako wasu da ake zargi da laifin kashe wata dalibar kwalejin ilimi ta Shehu Shagari Sokoto, Deborah Samuel. akan zagin Annabi Muhammadu (S A W).

Wasu matasa sun fito kan manyan titunan birnin Sokoto a safiyar ranar Asabar suna neman a sako wasu mutane biyu da ‘yan sanda suka kama bisa zargin kisan dalibar.

Wasu faya-fayan bidio da hotona sun nuna yadda ​​dalibai suka kashe tare kona Deborah a ranar Alhamis din da ta gabata bisa zargin ta da aikata sabo.

Muzaharar wacce aka fara gudanar da ita cikin lumana, ta fara ne a zagayen Zabirah Mall da misalin karfe tara na safe, kuma masu zanga-zangar wadanda ba su da yawa a lokacin suna dauke da alluna masu rubuce-rubuce daban-daban.

An samu labarin cewa an yada bayanai kan zanga-zangar da aka shirya yi a shafukan sada zumunta a daren Juma’a.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: