Jam’iyyar APC ta tara sama da Naira miliyan 29,000 daga sayar da fom din nagani ina so da kuma na tsayawa takara a zaben 2023

0 82

Jam’iyyar APC mai mulki ta tara sama da naira miliyan dubu 29 daga sayar da fom din nagani ina so da kuma na tsayawa takara a matakai daban-daban na masu neman tikitin tsayawa takara a zaben 2023.

Jam’iyyar mai mulki ta sanya farashin fom din takarar ta na shugaban kasa a kan Naira miliyan 100, yayin da ta kasa takarar gwamna a Naira miliyan 50, da sanata miliyan 20, da kuma miliyan 10 ga masu neman kujerar majalisar wakilai ta tarayya.

Sakataren jam’iyyar na kasa, Sulaiman Argungu, ya shaida wa manema labarai jiya a Abuja cewa, ‘yan takara 145 ne suka sayi fom din takarar gwamna, yayinda 351 suka fanshi fom din tsayawa takarar sanata, sai mutane 1,197 da suka karbi fom na majalisar wakilai, yayin da yayin da 28 ke neman takarar shugaban kasa suma suka sayi fom din a babban ofishin jam’iyyar na kasa.

Sakataren jam’iyyar Argungu ya ce an sanya ranar 23 ga watan Mayu domin tantance masu neman shugabancin kasar.

Jam’iyyar ta samu naira biliyan 2 da miliya 800 daga sayar da fom din takarar shugaban kasa ga ‘yan takara 28, naira biliyan 7.2 ga ‘yan takarar gwamna 145, naira miliyan 7 da ‘yan takarar sanata naira biliyan 7 da kuma naira biliyan 11.9 daga ‘yan takarar majalisar wakilai, wanda ya kai sama da naira biliyan 29 a jiya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: