Labarai

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kashe ‘yan sanda uku da wani dan achaba a garin Suleja na jihar Neja

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kashe ‘yan sanda uku da wani dan achaba a garin Suleja na jihar Neja.

An rawaito cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 11 na daren jiya.

Rahotanni sun ce ‘yan sandan na amsa kiran gaggawa ne a lokacin da aka yi musu kwanton bauna a kusa da wani wuri da ake kira Old Barracks.

Shugaban Karamar Hukumar Suleja, Alhaji Abdullahi Shuaibu Maje, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce kimanin mutane uku ne suka tsira daga harin, ciki har da dan kato da gora.

Ya ce yanzu haka suna jinya a wani asibiti da ke yankin.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Wasiu Abiodun, bai amsa kiran waya da sakon da aka aika masa dagane da batun ba.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: