Ministoci 10 ne suka yi murabus domin neman mukaman siyasa, biyo bayan umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari a taron majalisar zartarwa ta tarayya da ya gabata.

Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Muhammad, ya sanar da hakan ne a yau a lokacin da yake zantawa da manema labarai na fadar shugaban kasa bayan wani taro da aka gudanar a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Ya ce nan ba da jimawa ba za a maye gurbin ministocin da wasu.

Lai Mohammed ya bayyana sunayen tsoffin ministocin da suka halarci zaman wanda suka hada da Rotimi Amaechi, sufuri, Chris Ngige, kwadago da ayyukan yi, Godswill Akpabio, harkokin Neja Delta, Dokta Ogbonnaya Onu, Kimiyya da fasahar kere-kere da Timipre Sylva, karamin ministan albarkatun man fetur.

Sauran sune Tayo Alasoadura, karamin ministan Neja Delta, Dame Tallen Paulen, Al’amuran Mata, Uche Ogar, karamin ministan Tama da Karafa, Abubakar Malami, Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a da Emeka Nwajiuba, karamin ministan ilimi wanda bai samu halasta ba amma tare da izini.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: