Akalla Mutane 15 Ne Suka Mutu Wani Hatsarin Mota Da Ya Auku A Jihar Enugu

0 95

Akalla mutane 15 ne suka mutu wani hatsarin mota da ya auku a jihar Enugu.
A cewar wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin hakumar kiyaye aukuwar hadura ta kasa Bisi Kazeem yau Lahdi, yace hatsarin ya auku ne a sakamakon gudun wuce sa’a da kuma karya wasu dokokin tuki.
Hakumar ta shawarci direbobi masu tafiyar dare, inda tace jami’an ta a shirye suke domin magance hadura dake da alaka da gudun wuce sa’a.
Hatsarin ya auku ne da misalin karfe 8 da mintuna 20 na daren jiya, a kusa da asibitin koyarwa na jami’ar Najeriya dake Ituku a jihar Inugu.
Tsakanin wata mota kirar Toyota Hiace dauke da mutane 13 da wata Marsandi kirar Benz dauke da mutane 2 wanda duk sun mutu bayan motocin biyu sunyi arangama, inda suka kone kurmus.

Leave a Reply

%d bloggers like this: