Akalla mutane 360 ne aka kashe fadin jihar Kaduna daga watan Janairu zuwa watan Maris na 2022 a rikicin kabilanci da kuma ta’addanci

0 75

Kwamishinan tsaro da cikin gida na jihar Kaduna Samuel Aruwan, yace akalla mutane 360 ne aka kashe fadin jihar daga watan Janairu zuwa watan Maris na 2022 a rikicin kabilanci da kuma ta’addanci.

Kwamishinan ya bayyana hakan ne a lokacin dayake kaddamar da rahoton tsaro na watanni ukun farkon wannan shekarar ga gwamnan jihar Nasir El-Rufai a birnin Kaduna.

Ya kara da cewa a watanni ukun farkon wannan shekarar anyi garkuwa da mutane 1,389 da santoriyar birnin Kaduna.

Inda yace ansace mutane 165 a Birnin Gwari, sai mutum 158 a Giwa, sai kuma karamar hukumar Igabi da mutane 263, sai kuma Chikun 287 da kuma karamar hukumar Kajuru 203.

A cewar Aruwan an sace kimanin mutane 249 ne a kudancin Kaduna a wasu  hare-haren ta’addanci a yankin.

Haka mutanen da aka kashe a birnin Kaduna yan ta’addane suka kashe su.

Ya kara da cewa a cikin watannin ukun farkon wannan shekarar anyi garkuwa da wasu mata dayawa, tare da yiwa 10 daga cikin su fyade.

Leave a Reply

%d bloggers like this: