Majalissar dokokin jihar Yobe ta musanta zargin da ake mata, na yunkurin tsige gwamnan jihar Mai Mala-Buni.

Mataimakin shugaban kwamitin watsa labarai na majalissar Alhaji Abdullahi Bazuwa ne ya bayyana hakan a lokacin dayake karin haske a Damaturu babban birnin jihar, tare da karyata labaran yunkurin majalissar na tsige gwamna Mai Mala Buni daga kan mukamin sa.

Kafin hakan dai wasu kafafen yada labarai na yanar gizo sun wallafa cewa, majalissar dokokin jihar na yunkurin tsige mai Mala Buni daga mulkinsa.

Alhaji Abdullahi Bazuwa ya kuma bayyana cewa, yanzu haka majalissar ta maida hanakalinta ne wajan yin ayyukan tare da tabbbatar da kama jaridun da suka buga wannna labarin na kanzon kurege.

Tare da tsabbatar da cewa majalissaar zataci gaba da gudanar da ayyukan ta na yau da kullum kamar yanda aka saba.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: