Labarai

Fadar Shugaban Kasa ta ce ana cigaba da tattaunawa domin kubutar da mutanen da yan bindiga suka sace a hanyar Jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja

Fadar Shugaban Kasa ta ce ana cigaba da tattaunawa domin kubutar da mutanen da yan bindiga suka sace a hanyar Jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja, a farkon wannan shekarar.

Kakakin Shugaban Kasa Malam Garba Shehu, shine ya bayyana hakan, a lokacin da yake jawabi kan dakatar da jigilar Jirgin kasan da aka kuduri aniyar yi a baya.

Malam Garba Shehu, ya bayyana hakan ne a lokacin da ya bayyana a gidan Talabiji na Channels ta cikin shirin Politics Today, inda ya ce fadar shugaban kasa tana sane da damuwar da Iyalan mutanen da yan bindigar suke ciki.

Haka kuma ya ce gwamnati ta jajirce wajen tabbatar da cewa mutanen da suke hannun yan bindigar sun kubuta duk da cewa hakan zai yi wahala ta hanyar sansanto.

Malam Garba Shehu, ya ce gwamnati tana son abubuwa su lafa a hanyar Kaduna zuwa Abuja, inda ya ce ana samun cigaba a fannin harkokin tsaron yankin.

Kazalika, ya ce domin tabbatar da cewa hanyar ta samu ingantatcen tsaro, zai shiga cikin jirgin a duk lokacin da za’a fara Jigilar.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: