Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamido ya bukaci masu neman kujerar shugaban kasa su sanya bukatar Najeriya sama da tasu

0 57

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa kuma Jigo a Jam’iyar PDP Sule Lamido, ya bukaci masu neman kujerar shugaban kasa su sanya bukatar kasa a sama da tasu fiye da komai.

Sule Lamido, ya bayyana hakan ne a lokacin da yan takarar shugaban kasa karkashin Jam’iyar PDP wanda suka hada da Anyim Pius Anyim, da Bukola Saraki da kuma Atiku Abubakar suka kawo masa ziyara a gidan sa da ke Dutse.

Tsohon Gwamnan ya ce Jam’iyar APC ta jefa yan Najeriya cikin Mayuyacin hali, biyo bayan yadda suka samu gwamnati ba tare da shiri ba.

Lamido, ya ce yan Najeriya sun gamsu da cewa Jam’iyar PDP ce kadai wanda zata fitar musu kiste daga wuta.

Yan takarkarun shugaban kasar 3 sun shigo Jihar Jigawa ne domin neman kuri’ar Delegates a zaben fidda gwani da ke tafe.

Leave a Reply

%d bloggers like this: