Tsohon Gwamnan Jihar Ogun kuma dan takarar shugaban kasa a Jam’iyar APC Ibekunle Amosun, ya ce zai inganta fannin Noma a Jihar Jigawa matukar an zabe shi a matsayin shugaban kasa.

Sanata Amosun, ya bayyana hakan ne a taron masu ruwa da tsaki da kuma Delegates na Jam’iyar APC ta Jihar Jigawa da ke Dutse babban birnin Jiha.

Jihar Jigawa tana daya daga cikin Jihohin da ake noman Dabino a Gonaki.

Da ya ke bayyana kudurirrikansa, Mista Amosun ya ce matukar ya zama shugaban kasa, zai inganta Noman Dabino a Jigawa, inda ya kara da cewa Manoma kuma za su koyi sabbin dabarun Noma domin inganta fannin.

Tsohon Gwamnan Jihar ta Ogun, ya ce ya fito takarar shugaban kasar ne biyo bayan kiraye-kirayen da yan Najeriya suke yi.

A jawabin sa, Gwamna Muhammadu Badaru Abubakar, ya bayyana Amosun, a matsayin mutum mai Fikira wanda ya bada gagarumar gudunmawa wajen ciyar da Ogun gaba a lokacin da yake Gwamnan Jihar.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: