Akalla mutane 60 ne suka mutu sanadiyyar cutar amai da gudanawa a jihar Katsina

0 75

kwamishinan lafiya na jihar katsina, Yakubu Nuhu Danja, yace akalla mutane 60 ne suka mutu sanadiyyar cutar amai da gudanawa a jihar.

Ya sanar da haka a karshen mako a lokacin babban taron shekara-shekara na kungiyar likotoci ta kasa reshen jihar da aka gudanar a Katsina.

Nuhu Danja yace an samu mutane sama da dubu 1 da 400 da suka harbu da cutar ta kwalara a jihar, amma bai bayyana kananan hukumomin da lamarin ya shafa ba.

Sai dai, ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar na aiki domin dakile bazuwar cutar.

Ya bukaci mazauna jihar da su dauki matakan kariya ta hanyar tabbatar da tsafar jikinsu da ta muhallinsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: