An harbe wasu mutane 4 da ake zargin ‘yan fashin daji ne a jihar Kaduna

0 68

Jami’an tsaro a jihar Kaduna sun harbe wasu mutane 4 da ake zargin ‘yan fashin daji ne a yankin karamar hukumar Igabi ta jihar.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan, ya sanar da haka cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya.

Aruwan yace an kashe wasu gawurtattun ‘yan fashin daji a wani kwari a yankin.

Yace yan fashin dajin sun gamu da ajalinsu lokacin da sojoji suka far musu a wajen ta hanyar luguden jiragen yakin sama, a wani bangare na aikin hadin gwiwa tsakanin sojojin kasa da na sama akan maboyar ‘yan fashin daji da aka gano.

Yace an kashe wasu ‘yan fashin da dama a harin na sama da na kasa.

Aruwan tunda farko a ranar Asabar yace dakarun soji sun kashe wasu ‘yan fashin dajin su 3 a lokacin da suke dakile wani hari a karamar hukumar Zangon Kataf.

Leave a Reply

%d bloggers like this: