Za a gina sashen shugaban kasa a asibitin gwamnati dake fadar shugaban kasa

0 79

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayar da wajen da za a gina sashen shugaban kasa a asibitin gwamnati dake fadar shugaban kasa.

Babban sakataren fadar shugaban kasa, Umar Tijjani ya shaidawa ‘yan kwamitin majalisar dattawa cewa idan an kammala ginin sabon sashen asibitin fadar shugaban kasan, zai amfani ‘yan Najeriya.

Yace ginin asibitin na zamani, zai mayar da hankali wajen duba lafiyar shugaban kasa da mataimakinsa da iyalansu da kuma sauran jami’an gwamnati.

A cewarsa, ana sa ran kammala aikin cikin shekara 2, kafin karewar wa’adin gwamnatin Buhari.

Sai dai, Umar Tijjani ya koka dangane da kin sakin kudin dukkakin kudaden fadar shugaban kasa da aka ware a kasafin kudi, inda yace hakan ya zama kalubale kasancewar wasu daga cikin kayayyakin more rayuwa a fadar shugaban kasa basa aiki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: