Za a fara kaddamar da zagaye na biyu na rigakafin corona 16 ga watan Agusta

0 76

Kwamitin Shugaban Kasa na corona ya tsayar da ranar 16 ga watan Augusta domin kaddamar da zagaye na biyu na rigakafin corona.

Daraktan zartarwa na hukumar lafiya matakin farko ta kasa kuma mamba a kwamitin, Dr. Faisal Shuaib, ya sanar da haka a yau.

Aikin kaddamarwar, wanda ya kamata a gudanar a gobe, an dage shi a jiya da dare.

Tunda farko an shirya kaddamar da zagaye na biyu na rigakafin a cibiyar lafiya ta tarayya dake Jabi a Abuja.

Gwamnatin Amurka ce ta bayar da gudunmawar alluran rigakafin samfurin Moderna da za a ayi amfani da su a zagaye na biyun.

Kamar alluran rigakafin samfurin Astrazeneca, ana yin rigakafin Moderna ne sau biyu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: