Akalla mutane hudu ne suka jikkata biyo bayan fashewar tukunyar Gas a jiya

0 210

Lamarin ya faru ne a Ijaiye kusa da cocin Apostolic da ke Agege a jihar legas, inda aka gano wani shago ya kamata da wuta sakamakon tunkuyar da ta fashe.

A cewar wani rahoto da hukumar bada agajin gaggawa ta jihar LASEMA ta fitar, an gano cewa tukunyar  ce ta bule hakan ya haddasa kamawar wuta a shagon.

Koda ya ke ba’a samu rasa rai ba, amma mutane 4 da suka hada da mata uku da na Miji daya sun samu munanan raunuka sakamakon faruwar lamarin, inda yanzu haka suke samun kulawa a Asibiti. Daraktar hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Dr Olufemi Oke-Osanyitolu yace wanda lamarin ya rutsa da su, yanzu haka suna asibitin koyarwa na jami’ar Legas.

Leave a Reply

%d bloggers like this: