Akalla Yara Maza Da Mata 17 Ne Suka Mutu Sakamakon Kifewar Wani Jirgin Ruwa A Jihar Sokoto

0 105

Akalla yara maza da mata 17 ne suka mutu sakamakon kifewar wani jirgin ruwa da suke ciki a kogin Dandeji da ke karamar hukumar Shagari a jihar Sokoto.

Shugaban karamar hukumar, Aliyu Dantani, ya tabbatarwa kamfanin dillancin labarai na kasa afkuwar lamarin a Sokoto.

Ya ce hatsarin ya afku ne a jiya da safe, inda wasu masu shiga ruwa suka kwashe gawarwakin kuma aka binne su kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Shugaban karamar hukumar ya bayyana cewa, kimanin ‘yan mata da maza 40 ne ke kan hanyarsu zuwa debo itace a wani daji da ke kusa, lokacin da jirgin ruwan ya kife.

Ya ce wasu daga cikin fasinjojin sun yi iyo a ruwa inda suka tsira yayin da ake ci gaba da aikin neman wasu. Kamfanin Dillancin Labaran ya tunatar da cewa irin wannan lamari ya faru a ranar 13 ga Afrilun shekarar 2022 a kauyen Gidan Magana dake jihar inda mutane 29 galibinsu matasa suka mutu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: