Hukumar Sadarwa Ta Kasa (NCC) Ta Horar Sama Da Matasa 2,000 Kan Sana’o’in Fasahar Zamani

0 16

Sama da matasa dubu 2 daga shiyyoyi shida na kasar ne aka horar da su sana’o’in fasahar zamani a shirin samar da ayyuka ga matasa da Hukumar Sadarwa ta Kasa (NCC) ta gabatar.

Mataimakin shugaban hukumar Farfesa Umar Garba Danbatta, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a jiya, ya sanar da cewa ana horas da matasa 600 a shirin da ake ci gaba da gudanarwa.

A cewarsa, shirin samar da ayyukan yi na fasahar zamani ga matasa wani shiri ne da aka tsara domin inganta kwarewar matasa a shiyyoyin kasarnan 6 ta hanyar horar da su da kuma ba su kananan kwamfutoci dauke da na’urorin sadarwar zamani domin samar musu da kayan aiki bisa manufar shigar da su kasuwancin fasahar zamani daban-daban da za su zaba. Ya ce, wadanda suka ci gajiyar shirin, an samar musu da wuraren kwana kyauta na tsawon makonni biyu, inda masu hannu da shuni a fannin fasahar zamani, da bunkasa harkokin kasuwanci da sarrafa su suka himmatu wajen basu horo domin koya musu sanin kimar kansu da cigaban kansu da kansu, da kuma inganta rayuwarsu da kansu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: