El-Rufai Da Gwamnan Jihar Anambra, Charles Soludo, Sun Bukaci A Kawo Karshen Tsarin Tallafin Man Fetur

0 64

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, da takwaransa na jihar Anambra, Charles Soludo, sun bukaci gwamnatin tarayya da ta kawo karshen tsarin tallafin man fetur wanda ya yi illa ga tattalin arzikin Najeriya.

Gwamnonin sun yi magana ne jiya a Abuja a wajen taron siyasa da gabatar da littafi wanda da Dr. Zainab Usman, daraktar wani shiri na nahiyar Africa ta shirya.

Nasir El-Rufai ya jaddada bukatar kawo karshen tallafin man fetur.

Nasir El-Rufai ya kuma bayar da shawarar a sake fasalin tsarin rabon kudaden shiga na kasa domin amfanin jihohi.

Ya ce idan aka sauya fasalin rabon kudaden shiga zuwa kashi 20 na gwamnatin tarayya da kashi 80 na jihohi, to gwamnatin tarayya za ta mayar da mafi yawan ayyukanta da nauyin dake wuyanta a halin yanzu ga jihohi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: