Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi hasashen samun tsawa da ruwan sama daga Laraba zuwa Juma’a a faɗin Najeriya.
A cewar bayanai kan yanayi da hukumar ta fitar ranra Talata, ta ce ana sa ran samun tsawa a wasu sassan jihohin Borno, Adamawa, Taraba, Yobe, Katsina, Sokoto da kuma Kaduna ranar Laraba.
NiMet ta ce za a kuma samu tsawa a wasu ɓangarorin jihohoin Kano, Katsina, Kaduna, Zamfara, Kebbi da kuma Jigawa da rana da kuma yammaci.
“A arewa maso tsakiya, ana sa ran samun tsawa a Abuja, babban birnin tarayya, Nasarawa da kuma jihar Neja a ranar Laraban,” in ji NiMet.
Hukumar ta ƙara da cewa a yankin kudancin ƙasar ma za a fuskanci tsawa da ruwan sama a jihohin Oyo, Osun, Ekiti, Ogun, Ondo, Lagos, Edo, Delta, Cross River, da kuma Akwa Ibom daga Laraba zuwa Juma’a.
NiMet ɗin ta ce za a samu iska mai karfi kafin saukar ruwan saman a yankuna da dama, inda ta ja hankalin jama’a cewa su ɗauki matakan kariya da hukumomi suka fitar domin kare kansu.