Akwai yiwuwar Tinubu zai sauke wasu ministocinsa

0 95

Ana ci gaba da rade-radin cewar Shugaban kasa Bola Tinubu zai sauke wasu ministocinsa da ba su yi abun a zo a gani ba.

Wannan na zuwa ne bayan zaman majalisar zartaswa (FEC) da Shugaban kasar ya jagoranta a jiya Litinin.

Rahotanni da dama sun bayyana cewa Shugaban kasar na shirin yin wasu sauye-sauye nan ba da jimawa ba, bayan ya yi barazanar sallamar wasu ministocinsa da ba su taka rawar gani ba.

Duk da haka, shugaban bai tabbatar da takamaiman lokaci ko yadda sauyin zai gudana ba.

A taron majalisar, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ya jinjina wa Shugaban kasar kan rawar da ya taka wajen tabbatar da sahihin zaɓe a Jihar Edo.

Manyan jami’an gwamnati irin su Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkar Tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, da wasu ministoci sun halarci taron.

Sai dai hankali ya karkata kan yiwuwar Shugaban kasar na sauya ministocinsa a nan gaba kaɗan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: