Alhazan Najeriya Sun Karo Zauwa 36,199 A Saudiyya Domin Aikin Hajjin Bana

0 181

Yawan alhazan Najeriya a Kasar Saudiyya domin aikin hajjin bana ya karu zuwa 36,199, cikin jigilar jirage sawu 74.

An dai fara jigilar ne daga Najeriya ranar 10 ga watan da ya gabata na Yuli, bayan Hukumar Alhazai ta Kasa ta kaddamar da jigilar farko daga jihar Katsina.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa ya rawaito cewa, alhazan Najeriya na cigaba da tururuwa daga Madina zuwa Makkah, kuma ya zuwa yanzu sama da alhazai 25,000 sun isa Makkah.

Wakilin Hukumar Alhazai ta Kasa a Saudiyya, Dr. Tanko Aliyu, ya ce an kama otal otal guda 150 domin samawa alhazan matsugunnai a Birnin Makkah.

A wani cigaban kuma, Hukumar Alhazai ta Kasa ta yabawa tawagar yan jaridun Najeriya bisa abinda ta kira, jajircewa da sadaukar da kai wajen kawo rahotannin aikin hajjin bana a Saudiyya

Mataimakiyar Daraktar yada labarai ta Hukumar Alhazai ta Kasa, Hajiya Fatima Mustapha, ita tayi wannan yabon cikin wata sanarwa da aka fitar yau Asabar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: