Kwastam Tayi Alkawarin Samarwa Yan Gudun Hijira Kayan Abinci

0 113

Hukumr Hana Fasa Kwauri ta Kasa, Kwastan, tayi alkawarin samar da kayan abinci domin rabawa yan gudun hijirar da rikici ya raba da gidadejensu a jihar Bauchi, a cewar Mallam Isa Gusau, mataimakin Gwamna Babagana Zulum na Jihar kan yada labarai.

Mallam Isa Gusau ya jiyo Shugaban Hukumar Kwastan na Kasa, Kanal Hameed Ali (Mai Ritaya) na cewa, anyi nufin hakane domin saukaka musu radadin rayuwa.

A cewarsa, Hameed Ali, yayi alkawarin ne lokacin daya karbi bakuncin Gwamnan Zulum a Helkwatar Hukumar Kwastan dake Abuja ranar Juma’a.

An kuma jiyo Hameed Ali na cigaba da cewa, Hukumar ta Kwastan, tana bayar da gudunmawar kayan abinci ga yan gudun hijira a jihar Borno tun shekarar 2016, inda ya nuna cewa, akwai kyakykyawar alaka tsakanin hukumar tana da tsohon gwamnan jihar ta Borno, Kashim Shettima.

Tunda farko, Gwamna Zulum yace manufar ziyarar shine neman agaji kasancewar dubban manoma a yankin arewaci da tsakiyar jihar basa iya zuwa gonakinsu saboda fargaba da kuma ayyukan sojoji.

Sanarwar ta jiyo gwamnan na cewa sama da mutane 150,000 ne daga jihar ke samun mafaka a jamhuriyar Nijar da Kamaru.

Leave a Reply

%d bloggers like this: