Bayan Kai Ruwa Rana, Anyi Sulhu A Majalisar Dokokin Jihar Bauchi

0 108

A daren jiya Juma’a aka rantsar da sauran ‘yan majalisar dokokin jihar Bauchi su 17, a wani cigaban dake nuna da an samu cimma matsaya akan rikicin shugabancin da ya dabaibaye majalisar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa ya rawaito cewa, an kira zaman majalisar na musamman, da misalign karfe 9 na dare, wanda Mataimakin Kakakin Majalisar, Danlami Kawule, na jam’iyyar PDP, ya jagoranta. Inda aka rantsar da sauran yan majalisar da ba a rantsar da su a baya ba.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa ya labarto cewa, Kakakin Majalisar, Abubakar Suleiman na jam’iyyar APC, yana Abuja, a hanyarsa ta zuwa Saudiyya domin aikin Hajji.

Da yake jawabi bayan rantsuwar, Danlami Kawule, ya bukaci ‘yan majalisar da su aiki bisa dokar kudin tsarin mulki na Najeriya, da kuma dokokin majalisar.

Da yake magana da manema labarai jim kadan bayan rantsar da yan majalisar, Gwamnan Jihar ta Bauchi, Bala Mohammed, wanda ya halarci zaman majalisar, yayi godiya ga ‘yan majalisar bisa fahimtar juna.

Bala Muhammad yace, gwamnatin jiha, ta sasanta rikicin ta hanyar gudunmawar masu ruwa da tsaki, musamman sarakunan gargajiya.

Kawuwa Damina na jam’iyyar APC, wanda shine Kakakin Majalisar daya sauka baya-bayannan, wanda kuma yayi ta gabzawa a rikicin shugabanci da kakakin majalisar na yanzu, yana daga cikin wadanda aka rantsar, amma yaki cewa uffan ga manema labarai.

Majalisar dokokin jihar Bauchi ta yanzu, tana da ‘yan majalisa 31, kuma 22 daga ciki ‘yan jam’iyyar APC ne, sai 8 ‘yan jam’iyyar PDP dake mulkin jihar, da kuma wani 1 dan jam’iyyar NNPP.

Leave a Reply

%d bloggers like this: