Ali Ndume na Zargin Wasu Masu Zawarcin Kujerar Shugaban Majalisar Dattawa Ta 10 na Amfani kudi.

0 74

Sanatan Barnon ta kudu, Sanata Ali Ndume ya zargi masu zawarcin kujerar shugaban majalisar dattawa da siyan kuri’un wasu sanatoci yan uwan su.

Zababbun yan majalisar dattawan yanzu haka suna zawarcin shugabancin kujerar majalisar ta 10 gabanin rantsar dasu a watan Yunin wannan shekarar.Kazalika, Ndume ya zargi wasu sanatocin da amfani da kudi wajen neman goyan bayan yan uwan su sanatoci domin shugabantar majalisar.

Ali Ndume yace akwai sanatocin dake son zama shugabannin majalisar inda suke baiwa sanatoci kudi.Ya kuma kara da cewa wadannan mutane duk da yakai basu san aikin majalisa ba,saboda suna da kudi hakan yasa suke neman babban kujerar majalisar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: